<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>117</hymn_number>
<title>Yesu Kristi Yau Ya Tashi LW117</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Kristi yau ya tashi
 Ba zai sake mutuwa ba.
 Aka sa shi kabarinsa,
 Yau ya fashe sarƙarsa,
 Almasihu ba ya nan,
 Tashinsa ya tabbata.
 Jikinsa mai tsarki nc,
 Ba zai ruƃe ba daɗai

[V2]
 2) Yesu Kristi yau ya tashi.
 Shaidar nasara ya kai
 Cikin Sama wurin Allah,
 Yau har abada mai rai!
 Shi mai ɗaukar fansarmu,
 Ya isa mu yabe shi.
 Raɗaɗinsa duk ya wuce,
 Hau! ya kai Maɗaukaki !

[V3]
 3) Tuna, ku jama'ar Yesu,
 Haihuwarsa da mutuwa,
 Duba, ku rundunan Sama,
 Ga mutum, mai nasara!
 Shi kaɗai mai jiki ne
 Cikin Sama fa yanzu.
 Cikin jiki za mu sami
 Daraja har abada.</lyrics>
<author>Williams, Robert (1782-1818), Wesley, Charles (1707-1788)</author>
</song>